An sake yi mana zagon kasa a gasar zakarun Turai - AS Roma

Shugaban kungiyar AS Roma James Pallota.
Shugaban kungiyar AS Roma James Pallota. REUTERS/Tony Gentile/File Photo

Shugaban AS Roma James Pallota, ya ce an sake yiwa kungiyar tasa magudi wajen fitar da ita daga gasar Zakarun Turai ta bana, makamancin yadda aka yi mata a bara.

Talla

Pallota ya maida martani ne kan yadda alkalin wasa ya baiwa abokan hamayyarsu FC Porto damar bugun daga kai sai mai tsaron gida da bai cancanta ba, duk da cewa yayi nazarin matakin da taimakon fasahar maimaicin bidiyo.

A cewar Pallota, jim kadan itama Roma ta samu damar bugun, bayan tade dan wasanta Patrik Schick da aka yi a yadi na 16 dake gidan Porto, amma akalin wasa ya shafawa idanunsa toka ya ce a cigaba da wasa.

Matakin dai ya baiwa FC Porto damar fitar da Roma daga gasar zakarun turai ta bana, bayan samun nasara kanta da kwallaye 3-1 a wasan na ranar Laraba, a jimlace kuma tasamu nasara kanta ne da kwallaye 4-3, kasancewa a zagayen farko, AS Roma ce ta samu nasara kanta da kwallaye 2-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI