Wasanni

Guardiola yayi karin haske rahoton komawarsa Juventus

Mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola. REUTERS/David Klein

Mai horar da Manchester City Pep Guardiola, ya musanta rahotannin da ke cewa zai koma horar da kungiyar Juventus bayan kammala kakar wasa ta bana.

Talla

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata 8 ga watan Maris, gidan Rediyon CRC da ke Italiya ya bada rahoton cewa, Pep Guardiola ya cimma yarjejeniya da Juventus ta maye gurbin kocin kungiyar na yanzu, Massimiliano Allegri.

Sai dai lokacin da yake maida martani, Guardiola ya ce akwai yiwuwar ya sake kara wa’adin zamansa tare da Manchester City, idan yarjejeniyarsa da kungiyar ta kare nan da shekaru 2.

A cewar Guardiola zai rabu da Manchester City ne kawai idan kungiyar ta kore shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.