Wasanni

Dalilin Real Madrid na janye aniyar dawo da Mourinho

Jose Mourinho, tsohon mai horar da kungiyar Manchester United, Chelsea da Real Madrid.
Jose Mourinho, tsohon mai horar da kungiyar Manchester United, Chelsea da Real Madrid. Reuters

Tsohon shugaban Real Madrid Ramon Calderon, ya ce wasu jiga-jigan ‘yan wasan kungiyar ne suka hau kujerar naki dangane da yunkurin sake baiwa tsohon kocinsu Jose Mourinho damar horar da su kamar yadda aka yi zaton hakan baya.

Talla

Calderon ya jaddada cewa da fari shugaban Real Madrid Florentino Perez, Mourinho ya so yiwa tayin sake bashi dama, amma wasu ‘yan wasa suka yi barazanar rabuwa da kungiyar nan take, muddin aka baiwa Jose Mourinho damar.

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa ‘yan wasan da suka yi barazanar rabuwa da Real Madrid Muddin Mourinho ya dawo sun hada da Sergio Ramos, Gareth Bale, Marcelo da kuma Karim Benzema.

Idan za a iya tunawa dai, an yi ta samun sabani mai zafi tsakanin Ramos da Mourinho, a lokacin da ya horar da Real Madrid a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.