Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu Machester City karama ce a gasar Zakarun Turai - Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola.
Kocin Manchester City, Pep Guardiola. Reuters/Phil Noble Livepic
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Mai horar da Manchester City Pep Guardiola, ya bayyana shakku kan cewa kungiyar tasa za ta iya lashe kofin gasar Zakarun Turai na bana a karon farko.

Talla

Guardiola ya bayyana shakkunsa ne duk da cewa wasu daga cikin masu sharhi sun yi hasashen cewa City na daga cikin kungiyoyin da za su iya lashe gasar ta bana.

Guardiola ya bayyana mamakin yadda Manchester United ta fitar da PSG daga gasar Zakarun Turan, da kuma yadda Ajax fidda Real Madrid bayan lallasa ta da kwallaye 4-1 a Spain, sai dai ya ce fitar da manyan kungiyoyin, ba sharer fage bace ga Manchester City na saukaka mata damar zama zakarar nahiyar Turai a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.