Wasanni

Odion Ighalo ya ki amsa tayin komawa Barcelona

Dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo, yayin fafatawa da John Stones na Ingila, a wasan sada zumunci tsakanin Ingila da Najeriya a filin wasa na Wembley. 2/06/2018.
Dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo, yayin fafatawa da John Stones na Ingila, a wasan sada zumunci tsakanin Ingila da Najeriya a filin wasa na Wembley. 2/06/2018. REUTERS/David Klein

Dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo ya ce a watan Janairu da ya gabata, ya ki amsa tayin da kungiyar Barcelona ta yi masa na komawa fafata wasa a gasar La Liga ta Spain.

Talla

Da fari dai an sa ran Ighalo ba zai yi wasa da damar komawa wasa a Barcelona ba, amma ga mamakin da dama sai ya noke.

A wata zantawa da dan wasan yayi da manema labarai a baya bayan nan, Ighalo, y ace dalilansa na kin amsa tayin Barcelona sun hada da cewa, na farko kungiyar tayi masa ttayin komawa gareta ne a matsayin aro zuwa wani lokaci, zalika bashi da tabbacin kungiyar za ta rika bashi cikakkiyar dama ko lokacin buga wasanni ba.

Dan haka dan wasan ya zabi ci gaba da zama a gasar kwallon kafa ta China, sai dai ya sauya sheka daga tsohuwar kungiyarsa ta Changchun Yatai zuwa Shanghai Greenland Shenhua.

Rahotanni sun nuna cewa, a baya, Barcelona ta yi kokarin sayen Odion Ighalo ne saboda taimakawa dan wasanta nag aba Luiz Suarez, zalika Ighalo zai rika cike gurbinsa idan ya samu rauni, ko wata larurar da za ta hana shi bugawa kungiyar wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI