Wasanni

Giroud ya bayyana shirin rabuwa da Chelsea

Dan wasan gaba na Chelsea Olivier Giroud.
Dan wasan gaba na Chelsea Olivier Giroud. Reuters/John Sibley

Dan wasan gaba na Chelsea, Olivier Giroud, ya ce a shirye yake ya rabu da kungiyar a karshenkakar wasa ta bana, saboda matsalar da yace yana fuskanta ta ki bashi damar buga wasanni, karkashin kocin kungiyar ta Chelsea Maurizio Sarri.

Talla

Kalaman dan wasan na zuwa a dai dai lokacin da rahotanni ke cewa kungiyar Marseille da ke gasar League 1 ta Faransa na nemansa.

Giroud mai shekaru 32, ya soma zaman dumama benci ne bayan zuwan da Gonzalo Higuain yayi a matsayin aro daga kungiyar AC Milan.

Tauraruwar dan wasan na Giroud ta soma haskawa ne a shekarar 2012, bayan taimakawa kungiyar Montpellier lashe kofin gasar League 1 ta Faransa, inda a shekarar Arsenal ta saye shi, a watan Janairu na 2018 kuma dan wasan ya koma Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI