Wasanni

Tanzania za ta halarci gasar AFCON karon farko cikin shekaru 39

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Emmanuel Amunuke, ya samu nasarar jagorantar tawagar kwallon kafa ta Tanzania ga samun tikitin halartar gasar cin kofin nahiyar Afrika, karo na farko cikin shekaru 39.

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Emmanuel Amunuke dake horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Tanzania.
Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Emmanuel Amunuke dake horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Tanzania. Goal.com
Talla

Nasarar kasar ta Tanzania ta tabbata ne bayan lallasa Uganda da kwallaye 3-0 yayin wasan da suka fafata babban filin wasa da ke birnin Dar es Salaam, a jiya Lahadi.

Rabon Tanzania da samun irin wannan nasara tun a shekrar 1980.

Tanzani ta kammala rukunin da take ciki na 12 a matsayin jagorarsa yayinda Uganda ke biye da ita, hakan ya basu damar halartar gasar cin kofin nahiyar ta Afrika AFCON.

Wasu daga cikin kasashen da suka samu cancantar halartar gasar ta AFCON sun hada da Guinea Bissau, Namibia, Masar, Tunisia, sai kuma Ghana, da Kenya.

Sauran kasashen sun hada da Kamaru, Morocco, Angola, sai kuma Senegal, Madagascar, Mali, Algeria da Benin, yayinda Najeriya da Afrika ta Kudu ma suka bi sawu.

Ivory Coast, Zimbabwe, Jamhuriyar Congo da Guinea sun samu nasu tikitin, sai kuma Burundi, kasar da karon farko kenan za ta soma halartar gasar cin kofin ta nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI