Wasanni

Mbappe na gaf da zama dan wasa mafi tsada a duniya

Kylian Mbappe dan kasar Faransa.
Kylian Mbappe dan kasar Faransa. Reuters

Bayan shafe tsawon lokaci ana yada rahotannin cewa Real Madrid za ta sayi dan wasan PSG Kylian Mbappe, daga karshe dai Kocin kungiyar ta Real Madrid Zinaden Zidane a hukumance, ya bayyana bukatar sayo dan wasan.

Talla

Majiya sahihiya ta rawaito cewa tuni Zidane ya mikawa shugaban kungiyar ta Real Madrid Florentino Perez kudurin.

A hali da ake ciki kuma, rahotanni sun ce, Real Madrid a shirye take ta biya PSG euro miliyan 280 domin sayen Kylian Mbappe mai shekaru 20, dake rike da kyautar Gwarzon dan kwallon kafa na duniya a ajin matasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.