Wasanni

Pogba zai nemi albashi mafi tsoka a Real Madrid

Paul Pogba dake Manchester United zai bukaci albashi mafi tsoka daga duk kungiyar da ta yi masa tayin komawa gareta a hukumance, tsakanin Real Madrid da Juventus, a karshen kakar wasa ta bana.

Paul Pogba.
Paul Pogba. Reuters
Talla

Wakilin Pogba, Mino Raiola ne ya bayyana haka yayin sanar da adadin kudaden da suka tsaida a matsayin albashin da zai nema daga duk kungiyar da tayi kokarin sayen dan wasan na Tsakiya.

A cewar Raiola, Paul Pogba na neman albashin euro miliyan 16 a duk shekara, kwatankwacin kusan fam din Ingila dubu 300 a kowane mako.

Raiola ya jaddada aniyar ganin Pogba ya zama dan wasa mai daukar albashi mafi tsoka a Real Madrid muddin yarjejeniya ta kullu tsakaninsu.

A halin yanzu dai babu dan wasan da yakai Sergio Ramos da Gareth Bale daukar albashi mai tsoka a kungiyar ta Real Madrid.

Gareth Bale na karbar euro miliyan 14 a shekara, yayinda Sergio Ramos ke karbar euro miliyan 11.

A Manchester United dai Paul Pogba na karbar euro miliyan 10 a matsayin albashi na shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI