wasanni

Ko Liverpool za ta lashe kofin firimiyar Ingila?

Mohamed Salah ne ya buga kwallon da Alderweireld ya ci gida
Mohamed Salah ne ya buga kwallon da Alderweireld ya ci gida Reuters/Paul Childs

Kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya ce, kungiyar na farfado da damarta ta lashe kofin firimiyar Ingila a bana bayan nasarar da ta samu akan Tottenham da ci 2-1, abinda ya sa ta sake cillawa can saman teburin gasar.

Talla

Kwallon da Toby Alderweireld ya ci gida ana gab da tashi wasan ne, ta bai wa Liverpool wannan nasarar, yayinda Roberto Firmino ya ci wa Liverpool din kwallon farko a minti na 16, in da Lucas Moura ya ci wa Tottenham kwallonta daya tilo a minti na 70.

A halin yanzu Tottenham ta tsindima cikin tsaka mai wuya domin kuwa tana fuskatar gagarumar barazanar rasa gurbi a matakin ‘yan hudun saman teburi, lura da cewa, ta yi kan-kan-kan da Manchester United wajen yawan maki, in da kowacce daga cikinsu ke da maki 61 a teburin, sannan kuma Arsenal za ta iya kwace mata matsayi muddin ta doke New Castle a karawar da za su yi a yau Litinin.

A bangare guda, ‘yan wasan Liverpool na fatan Manchester City da ke matsayi na biyu a teburi, ta yi barin maki a sauran wasanni bakwai da suka rage mata.

Liverpool mai jan ragamar teburin na da maki 79, yayinda Manchester City da ke matsayi na biyu ke da maki 77.

Shekaru 29 kenan raban da Liverpool ta dauki kofin firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI