Ronaldo zai yi jinyar sama da makwanni 6
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga kasar Italiya sun tabbatar cewa tauraron dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo, zai jinyar makwanni takwas, kafin dawowa wasa.
A karshen watan Maris da ya gabata, Ronaldo yasamu rauni a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin nahiyar Turai, da kasarsa Portugal ta buga da Serbia, wanda suka tashi 1-1.
Hakan na nufin Ronaldo ba zai damar buga wasanni biyu da Juventus za ta fafata da Ajax ba a zagayen kwata final na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.
Zalika Ronaldo ba zai buga wasanin gasar Seria A da Juventus za ta fafata da kungiyoyin Cagliari, AC Milan, SPAL, Forentina, Inter Milan, Torino, AS Roma, Atalanta da kuma Sampdoria ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu