wasanni

Arsenal ta kado Tottenham daga teburin firimiya

Kocin Arsenal, Unai Emery ya jinjina wa Mesut Ozil kan rawar da ya taka a wasansu da Newcastle a Emirates
Kocin Arsenal, Unai Emery ya jinjina wa Mesut Ozil kan rawar da ya taka a wasansu da Newcastle a Emirates Reuters / Dylan Martinez

Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal ta doke Newcastle a Emirates da ci 2-0, nasarar da ta ba ta damar darewa saman Manchester United da Tottenham a teburin gasar firimiyar Ingila, in da a yanzu take a matsayi na uku biye da Liverpool da Manchester City da ke matsayi na daya da na biyu.

Talla

Aaron Ramsey ne ya fara ci wa Arsenal kwallonta ta farko a minti na 30, kafin Alexandre Lacazette ya kara ta biyu a minti na 83.

A farkon watan Fabairun da ya gabata, Tottenham ta bai wa Arsenal tazarar maki 10 a teburin gasar, amma wannan nasarar da ta samu akan Newcastle ta sa a yanzu, Arsenal din ta kere wa Tottenham da Manchester United da maki 2.

Arsenal na da maki 63, yayinda Tottenham da Manchester United kowacce ke da maki 61.

A karo na 10 kenan a jere da juna da Arsenal ke samun nasara a wasannin da ta yi a gidanta na Emirate a gasar Lig, kuma raban da ta nuna irin wannan bajintar tun a watan Disamban 1997 da kuma watan Mayun 1998.

Kungiyar ta kama hanyar nemawa kanta gurbi a gasar zakarun nahiyar Turai bayan ta shafe shekaru biyu ba tare da samun tikitin halartar babbar gasar a Turai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.