Real Madrid za ta sauya fasalin Santiago Bernabéu
Wallafawa ranar:
Shugaban Real Madrid Florentino Perez, ya ce kungiyar za ta sauya fasalin filin wasanta na Santiago Bernabéu a karshen kakar wasa ta bana.
Perez ya ce sauya fasalin filin wasan zai lashe adadin kudin da ya kai kimanin dala miliyan 560.
Aikin dai zai shafi suya fasalin rufin filin na Santiago Bernabeu, da kuma taswirar filin da ake shafa tamaula a kansa, sai kuma sauya fasalin ginin filin wasan daga waje.
Shugaban na Real Madrid ya ce bayan kammala gayaran filin, kungiyar na sa ran samun karuwar kudaden shiga da adadin dala miliyan 168 a shekara guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu