Wasanni

Chelsea ta bayyana dan wasan da zai maye gurbin Hazard

Dan wasan Barcelona Philippe Coutinho.
Dan wasan Barcelona Philippe Coutinho. REUTERS/Albert Gea

Kungiyar Chelsea ta ce a shirye take ta biya euro miliyan 142, wajen sayen Philippe Coutinho daga Barcelona, domin maye gurbin dan wasanta Eden Hazard.

Talla

Rahotanni sun ce, Chelsea na fatan sayen Coutinho ne, da kudaden da Real Madrid za ta mika mata bayan sayen dan wasanta Eden Hazard, cinikin da ake sa ran zai tabbata a karshen kakar wasa ta bana.

An dai shafe watanni ana takara tsakanin Chelsea da Manchester United kan sayen Coutinho daga Barcelona.

Wata majiya dake kusa da Coutinho ta ce tuni dan wasan ya shaidawa takwarorinsa a Barcelona cewa, yana sa ran rabuwa da kungiyar a karshen kakar wasa ta bana.

Sai dai sayen Coutinho ba zai yiwu ga Chelsea ba a halin yanzu, har sai FIFA ta dage mata takunkumin sayen ‘yan wasan da ta kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.