Wasanni

Messi ya zarta takwarorinsa wajen samun kudi

Wani rahoto da hukumar kwallon kafa ta Faransa ta fitar, ya nuna cewa kaftin din kungiyar Barcelona kuma dan kasar Argentina Lionel Messi, shi ne yafi kowane dan wasan kwallon kafa karbar albashi.

Lionel Messi.
Lionel Messi. Sergio Perez/Reuters
Talla

Rahoton dai yayi la’akari ne da jimillar kudaden da ‘yan kwallon kafa ke samu daga albashi, da sauran kudaden shigar da suke samu daga yarjejeniyar talla da suke kullawa da manyan kamfanoni.

Hukumar kwallon ta Faransa ta ce a shekara guda ana biyan Messi euro miliyan 130.

Yayinda Cristiano Ronaldo dake Juventus, ke biye da shi a matsayi na biyu, inda yake samun euro miliyan 113, sai kuma dan wasan PSG Neymar a matsayi na uku, wanda ke samun adadin kudin da ya kai euro miliyan 91 da dubu 500 a shekara guda.

Sauran ‘yan wasan sun hada da Antoine Griezmann na Atletico Madrid da ke samun euro miliyan 44 a shekara, yayinda Gareth Bale na Real Madrid ke samun euro miliyan 40 da dubu 200 a matsayi na 5.

Adadin ‘yan wasa 20 ne dai aka bayyana matsayi ko matakin da suke kai, dangane da yawan albashi, da kudaden da suke samu daga talla a tsawon shekara guda.

Matashin dan wasa Kylian Mbappe na daga cikin 'yan wasan guda 20, inda yake kan matsayi na 14, tare da samun euro miliyan 25 a shekara guda.

Paul Pogba na Manchester United ne na 19 wanda ake biya euro miliyan 23 da dubu 300 a shekara, sai Sergio Ramos na Real Madrid a mataki na 20, wanda ke samun euro miliyan 23 daidai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI