wasanni

Chelsea ta sha gaban Arsenal da Tottenham

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta casa West Ham United da ci 2-0, abinda ya ba ta damar shan gaban Tottenham da Arsenal a teburin gasar firimiyar Ingila, in da yanzu take a matsayi na uku a teburi.

Dan wasan Chelsea Eden Hazard.
Dan wasan Chelsea Eden Hazard. Reuters / Stefan Wermuth Livepic
Talla

Eden Hazrd da ake alakanta shi da komawa Real Madrid a Spain, shi ne ya ci wa Chelsea dukkanin kwallayen biyu a minti na 24 da kuma minti na 90.

A bangare guda, kocin Chelsea, Maurizio Sarri ya bayyana cewa, abu ne mai wahala su hana Hazard komawa Real Madrid a cikin wannan kakar, duk da dai  farashinsa na Euro miliyan 100 ya yi araha a cewar kocin.

Kocin ya ce, Chelsea ba ta son sayar da Hazard amma dole ne su mutunta muradinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI