wasanni

Ko Tottenham ta shirya karawa da Manchester City?

Yau ne kungiyar kwallon kafa ta Tottenham za ta karbi bakwancin Manchester City a sabon filinta da ta gina a kan Pam biliyan 1 a Gasar Zakarun Turai

Tambarin Gasar Zakarun Turai
Tambarin Gasar Zakarun Turai Reuters
Talla

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino ya ce, wannan karan-battan da za a yi tsakanin kungiyoyin biyu, na daya daga cikin wasanni mafi muhimmanci a tarihinsa na horar da tamaula.

Kodayake kocin ya ce, babu makawa, kece- rainin zai yi zafi sosai, lura da cewa, Manchester City na cikin zamaninta.

Ana ganin watakila Manchester City ta kafa tarihin lashe kofuna hudu a wannan kaka, amma kocinta, Pep Guardiola ya ce, abinda kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa.

Tuni ta lashe kofin Carabao, sannan tana fatan lashe kofunan firimiyar Ingila da na gasar FA da kuma na gasar zakarun Turai.

Ita ma Liverepool za ta karbi bakwancin FC Porto a Anfield a matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar ta cin kofin zakarun Turai.

Akwai yiwuwar Liverpool ta casa FC Porto, musamman idan aka yi la’akari cewa, a kakar bara, ta doke Porto da jummular kwallaye 5-0 a zagaye na biyu na gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI