Wasanni-kwallon kafa

Kane zai iya kai karshen kakar wasa ya na jinya- Pochettino

Harry Kane
Harry Kane REUTERS/Carlos Barria

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino ya ce akwai yiwuwar raunin Harry Kane ya kai shi har zuwa karshen kakar wasan nan bai murmure ba ko da dai ya ce suna fata idan likitoci sun duba ya zama ba babbar matsala ba ce.

Talla

Kane ya samu raunin ne a wata taho-mu-gama da suka yi da Fabian Delph a wasan jiya wanda Tottenham din ta lallasa Man city da kwallo daya mai ban haushi.

A cewar manajan raunin na Kane abin takaici dai dai lokacin da su ke fatan karkare kakar a matsayin ko dai na 3 ko kuma na 2 a gasar Firmiya, baya ga fatansu na ganin sun kai wani mataki a gasar zakarun Turai.

Ko cikin watan Janairu ma Kane dan Ingila ya gamu da makamancin raunin a wasansu da Man United amma kuma duk da haka Club din bai yi rashin nasara a ilahirin wasanninsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.