Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Manajan Ajax ya sha alwashin lallasa Juventus har gida

'Yan wasan Juventus bayan nasarar Ronaldo ta zura kwallo 1 a ragar Ajaz cikin minti na 41 da fara wasa
'Yan wasan Juventus bayan nasarar Ronaldo ta zura kwallo 1 a ragar Ajaz cikin minti na 41 da fara wasa Piroschka van de Wouw/Reuters

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Ajax Erik Ten Hag ya ce ya na da kwarin gwiwar zarrar lallasa Juventus a wasan makon gobe, wato zagaye na biyu na wasannin dab da na kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai, duk da cewa sun yi canjaras jiya kwallo 1-1 har gida.

Talla

A cewar kocin, Ajax na da tawagar ‘yan wasan da za su iya lallasa Juventus wadanda kuma ke da karsashin kai wa karshen gasar don dage kofin.

Manajan na Ajax, Erik Hag, ya ce ko a zagayen kungiyoyi 16 lokacin da suka kara da Real Madrid, Madrid din ta zura musu kwallaye 2 da 1 har gida, amma kuma suka farke tare da fitar da Madrid din a zagaye na biyu na wasan har gidanta.

Yayin wasan na jiya Laraba dai Cristiano Ronaldo ne ya zurawa Ajax kwallo a raga a minti na 41 da fara wasa gab da tafiya hutun rafin lokaci, yayinda David Neres ya farke cikin kasa da minti 1 da dawowa daga hutun na rabin lokaci.

Kwallon ta jiya dai ita ce kwallo ta 125 da Ronaldo dan Portugal mai shekaru 34 ya zura a gasar ta cin kofin zakarun Turai, inda ya ke tunkarar nasarar lashe kofin karo na 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.