wasanni

Maradona ya yi wa Pele fatan samun sauki

Tsohon gwarzon dan wasan Argentina, Diego Maradona ya yi wa takwaransa na Brazil, Pele fatan samun lafiya cikin gaggawa, in da ya wallafa hoton da suka dauka shekaru 40 da suka wuce a shafinsa na Intagram.

Maradona da Pele
Maradona da Pele PATRICK KOVARIK / AFP
Talla

Maradona ya ce, sun dauki hoton ne da Pele a Rio de Janeiro lokacin da suke matasa.

Hoton ya nuna Maradona mai shekara 18 a wancan lokaci cikin annashuwa yana kallon Pele da a wancan lokacin ke da shekaru 38, yana kada jita.

Ana kallon zaratan biyu a matsayin masu hamayya da juna, ganin yadda kowanne daga cikinsu ke kallon kansa a matsayin babban gwarzon da babu kamarsa a tarihin kwallon kafa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI