Jadawalin kasashen da za su kara a gasar cin kofin Afrika

Sauti 10:06
Wurin bikin fitar da jadawalin Gasar Cin Kofin Kasashen Afrika a birnin Al-Kahira na Masar
Wurin bikin fitar da jadawalin Gasar Cin Kofin Kasashen Afrika a birnin Al-Kahira na Masar KHALED DESOUKI / AFP

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi nazari ne game da jadawalin kasashen da za su fafata da juna a Gasar Cin Kofin Kasashen Afrika da kasar Masar za ta karbi bakwanci daga ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli. A karon farko kenan da kasashe 24 ke karawa a wannan babbar Gasar Kwallon Kafa a nahiyar. Wasu masana na ganin cewa, sabbin kasashen da suka shiga gasar a bana za su iya bada mamaki.