Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Ajax ta lallasa Juventus da kwallaye 2 da 1 har gida

Cristiano Ronaldo na Juventus
Cristiano Ronaldo na Juventus Marco BERTORELLO / AFP

Kungiyar kwallon kafa ta Ajax ta yi nasarar fitar da Juventus daga gasar ta zakarun Turai bayan zura mata kwallaye 2 a raga har gida.

Talla

A wasan na jiya dai Juventus ce ta fara nasarar zura kwallon farko, ta hannun dan wasanta Cristiano Ronaldo cikin minti na 28 da fara wasa, kafin daga bisani Ajax ta farke ta hannun dan wasanta Donny van de Beek ka na kuma ta kara kwallo na 2 a minti na 67 da fara wasa amma kuma Juve ta kasa farkewa har zuwa karshen wasa.

Yayin wasan na jiya dai, alkalin wasa Clement Turpin ya bai wa Emre Can da Cristiano Ronaldo katin gargadi dukkaninsu ‘yan wasan Juventus, lokacin da ake gab da karkare wasa.

An dai ta shi wasan na jiya da jumullar kwallaye 5 da 3, wato Ajax na da kwallonta daya data zura a Amsterdam da kuma 2 wadanda ke matsayin 4 da ta ratatawa Juve a jiya.

Za a iya cewa Juventus wadda ke fama da kishirwar Kofin zakarun Turai, wanda saboda shi ne ma ta siyo Ronaldo daga Real Madrid a kakar bara, sai dai fa ta tara kaka mai zuwa don sabon shiri.

A bangare guda ita kuma Ajax za a iya cewa a wannan karon za ta iya kai wa wasan karshe musamman la’akari da yadda ta lallasa Real Madrid mai rike da kambu kana a jiyan ta kara lallasa Juventus mai dauke da Ronaldo, dan wasa mafi zura kwallo a gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI