wasanni

Dan wasan Liverpool na tsoron Lionel Messi

Dan wasan baya na Liverpool, Virgil van Dijk ya bayyana cewa, shi kadai ba zai iya tunkarar Lionel Messi na Barcelona ba a wasan da za su yi nan gaba a matakin wasan dab da na karshe a Gasar Zakarun Turai.

Lionel Messi na Barcelona
Lionel Messi na Barcelona Reuters/John Sibley Livepic
Talla

Van Dijk ya yi amanna cewa, akwai bukatar hada karfi da karfe kafin tare Messi wanda ya zura kwallaye har guda 45 a wannan kakada suka hada da kwallayen da suka taimaka wajen fitar Manchester United daga gasar ta zakarun Turai.

A cewar Van Dijk, Messi ne gwarzon dan wasan duniya amma dai a zura idanu don ganin yadda za ta kaya a wasan nasu da ya ce, zai kasance na hamayya.

Van Dijk na cikin ‘yan wasan da ke takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan bana a Ingila, yayinda ya kasance mai tsaren baya mafi tsada a duniya, in da Liverpool ta saye shi daga Southampton akan farashin Pam miliyan 75 a cikin watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI