Wasanni

Liverpool ta fitar da FC Porto daga gasar zakarun Turai

Mohammad Salah bayan nasararsa ta zura kwallo a wasan na jiya wanda aka tashi kwallaye 4 da 1
Mohammad Salah bayan nasararsa ta zura kwallo a wasan na jiya wanda aka tashi kwallaye 4 da 1 Reuters/Paul Childs

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasarar fitar da takwararta ta FC Porto daga gasar cin kofin zakarun Turai a zagaye na biyu na wasan gab da na kusa da na karshe da ya gudana tsakanin kungiyoyin biyu a gidan Porto.

Talla

Yayin wasan na jiya wanda aka tashi Liverpool na da kwallaye 4 Porto kuma na da 1, Sadio Mane ne ya fara zura kwallon na farko cikin minti na 26 da fara wasa yayinda kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Mohammad Salah ya kara na biyun a minti na 65 yayinda a minti na 69 Eder Malitio na Porto ya farke, ko da dai daga bisani Roberto Firmino ya kara zurawa Liverpool kwallonta na 3 a ragar Porto ka na kuma Virgil van Dijk ya rufe da kwallo na 4 a minti na 84 gab da karkare wasa.

Dama dai tun a zagayen farko da ya gudana a gidan Liverpool Porton ta gaza, zura kwallo ko guda yayinda aka tashi wasa Reds na da kwallaye 2 da banza a ragar Porto.

Bayan gagarumar nasarar ta Liverpool a wasan, kai tsaye yanzu Liverpool din za ta tunkari, Barcelona a wasanta na gab da na karshe, wasan da ake ganin zai fi daukar hankali a cikin wasanni biyu na gab da na karshe na cin kofin na zakarun Turai, la’akari da cewa Barcelona fa ba kanwar lasa ba ce, ko da dai itama Liverpool kofin ba bakonta ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI