Wasanni-kwallon kafa

Tottenham ta shafe fatan Manchester City na lashe gasar Zakarun Turai

Dan wasan Tottenham Son Heung-Min bayan nasarar shi ta zura kwallaye 2 cikin minti 4
Dan wasan Tottenham Son Heung-Min bayan nasarar shi ta zura kwallaye 2 cikin minti 4 Paul Childs/Reuters

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta yi waje da Manchester City daga gasar ta cin kofin zakarun Turai bayan da aka tashi wasa Cityn na da kwallaye 4 Tottenham na da 3, amma da ya ke akwai kwantan kwallon guda da Tottenham ta zurawa Cityn ka na kuma a gidan Cityn aka yi wasan na jiya, haka ya sa Tottenham ta yi gagarumar nasarar.

Talla

Manchester City dai ta shiga fili a jiyan da karsashi, inda Raheem Sterling ya zura kwallon farko a ragar Spurs cikin minti na 4 da fara wasa, ko dai Heung-Min Son ya farke bayan minti 3 har ma da karin kwallo guda, yayinda shi ma Benardo Silva na Cityn ya kara kwallo na 2 ka na Sterling ya kara kwallo ta 3 a minti na 21 da fara wasa, wanda daga nan ne kuma aka tafi hutun rabin lokaci.

Ko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci dai sai da Sergio Aguero ya sake zurawa Tottenham kwallo guda a minti na 59 yayinda Fernando Llorente ya zurawa Tottenham din kwallonta na 3 a ragar City a minti na 73.

Yanzu haka dai Tottenham za ta tunkari Ajax ne wadda ta fitar da Juventus daga gasar a wasan gab da na karshe, wanda kuma idan har ta yi nasara ne za ta je ta hadu da ko dai Liverpool ko kuma Barcelona a wasan karshe.

Dama dai Manajan City Pep Guardiola ya koka da yadda ya ce Tottenham ta zame masa karfen kafa a gasa har biyu manya da ya ke fatan lashewa a wannan kaka, wato Firimiya da Zakarun Turai.

Sai dai fa duk da shan kayen na City a hannun Tottenham, ranar Asabar ma, Spurs din za ta kara tattaki gareta karkashin gasar Firimiya wanda shi ma wasan ne zai fayyacewa City ko za ta kai labari a gasar ta Firimiya ko akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI