Wasanni-kwallon kafa

Solskjaer ya nemi yafiyar magoya bayan Manchester United

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer Svein Ove Ekornesvaag / NTB SCANPIX / AFP

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya nemi yafiyar magoya bayansu kan rashin nasararsu a hannun Everton jiya Lahadi da kwallaye 4 da banza.

Talla

Rashin nasarar ta United fami ne ga magoya bayanta akan kayen da Barcelona ta yi mata cikin makon jiya tare da fitar da ita daga gasar cin kofin zakarun Turai.

A cewar Ole Solskjaer, abubuwa sun tafi ba yadda suka yi fata ba tun daga fara kwallon har aka kammala, don haka dole ne su nemi yafiyar magoya baya, wadanda ya ce sun fi su jin radadin rashin nasarar.

Manajan ya ce a wasan na jiya Everton ta musu zarra a komi hatta a karsashin ‘yan wasansu wanda ya ce ya zama dole su samar da gyara don tunkarar wasansu na gaba da za su kara da Manchester City a cikin makon nan, wanda ya ce suna fata su cirewa magoya bayan nasu kitse a wuta ta hanyar lallasa Cityn har gida.

Bayan rashin nasarar ta jiya da kwallaye 4 da banza, hakan na nuna cewa kenan Unite ta sha kaye a wasanni 6 cikin 8 da ta doka a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI