Wasanni-kwallon kafa

Dan wasan Liverpool ya nuna goyon baya ga Manchester United

Wasu 'yan wasan Liverpool yayin murnar nasarar zura kwallo a raga
Wasu 'yan wasan Liverpool yayin murnar nasarar zura kwallo a raga Reuters/Carl Recine

Dan wasan Liverpool James Milner, ya ce a karon farko cikin tarihin rayuwarsa zai kasance mai goya baya ga Manchester United a wasan da za ta kara da Manchester City gobe Laraba, karkashin gasar Firimiya.

Talla

A cewarsa duk da cewa nasara ko rashin nasarar City ba zai hana su dage kofin Firimiyar ba, amma dai ya na fata Cityn ta sha kaye a wasan.

Liverpool wadda yanzu ke matsayin jagora da maki 88 bayan doka wasanni 35 ta dara City wadda ke matsayin ta 2 da maki 86 ko da dai ita wasanni 34 kadai ta buga inda a goben ne za ta buga na 35 tare da United, kuma matukar ta yi rashin nasara a wasan ana ganin kai tsaye ta rasa damar dage kofin yayinda Liverpool za ta iya kawo karshen kishirwwarta ta rashin kofin tsawon shekaru 29.

Yanzy haka dai wasanni 3 suka ragewa Liverpool din kuma ana ganin dukkansu masu sauki ne wato tsakaninta da Huddersfield, ka na da Newcastle sai kuma na karshe da Wolverhampton Wanderers, ko da dai James Milner ya ce a gasar Firimiya babu wasa mai sauki.

A bangare guda ita kuma City bayan karawarta ta ta gobe da Manchester United, akwai ita ma wasanni 3 da suka kunshi wanda za ta kara da Burnley haka da Liyasta sai kuma wasan karshe da Brighton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI