Mbappe ya nesanta kansa da jita-jitar komawa Real madrid

Dan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe bayan zura kwallaye 3 a ragar Monaco
Dan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe bayan zura kwallaye 3 a ragar Monaco REUTERS/Gonzalo Fuentes

Dan wasan gaba na PSG da ya dage kofin duniya, Kylian Mbappe, ya nesanta kansa da jita-jitar da ke cewa ya na shirin sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a kakar wasa mai zuwa.

Talla

Mbappe wanda ya taimakawa PSG dage kofin Lig 1 karo na 6 bayan kwallaye har 3 da ya jefa a ragar Monaco, ya ce a yanzu ba ya tunanin sauya sheka, sai dai ya na yiwa Madrid murnar dawowar Zidane.

Tsawon lokaci dai ana jita-jitar cewa Madrid din za ta sayi wasu manyan ‘yan wasa na duniya ciki har da shi Mbappe da kuma Hazard wanda shit uni Club din ya ce shirye-shirye sun yi nisa.

Ko a wani taron manema labarai da shugaban Real Madrid Fiorentina Ferez ya kira cikin watan jiya, bayan dawowar Zidane fagen horar da Club din, ya shaidawa manema labarai cewa ya na son sayo Mbappe da kuma Neymar dukkaninsu ‘yan wasan PSG.

Madrid din dai ka iya fuskantar kamfar ‘yan wasa musamman idan ta tabbata Gareth Bale ya sauya sheka, wanda ake ganin shi ne ya dan cike gurbin Cristiano Ronaldo da ya sauya sheka daga Club din a kakar wasan da ta gabata.

Cikin Kaka guda dai sau 3 Real Madrid na sauya mai horarwa, yayinda suka yi ficewar wuri a gasar cin kofin zakarun Turai duk da kasancewarsu masu rike da kofin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.