Akwai yiwuwar Barcelona ta lashe kofin La Liga a yau
Wallafawa ranar:
Kungiyar Kwalon Kafa ta Barcelona na kara jin kamshin lashe kofin gasar La Liga ta Spain bayan da ta doke Alaves da ci 2-0 a karawarsu ta ranar Talata.
Wannan nasarar na nufin cewa, Barcelona za ta dage kofin muddin Atletico Madrid ta yi rashin nasara a hannun Valencia a yau Laraba.
Idan kuma Atletico Madrid ta yi nasara akan Valencia, to babu shakka Barcelona za ta dage kofin a ranar Asabar mai zuwa muddin ta doke Levente a Camp Nou.
Akwai tazarar maki 12 tsakanin Barcelona mai rike da kambi da kuma Atletico Madrid wadda ke da sauran wasanni biyar da suka rage mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu