"'Yan wasan Manchester City mugaye ne"
Wallafawa ranar:
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya gargadi ‘yan wasansa da su shirya shan maka daga ‘yan wasan Manchester City a karawar da za su yi yau a Old Trafford, kalaman da suka bai wa Pep Guardiola mamaki, ganin yadda takwaransa ya alakanta ‘yan wasansa da mugunta.
Solskjaer ya ce, za a yi wa ‘yan wasansa mugunta ta hanyar dukan kafafunsu a karawar, sai dai Guardiola bai ji dadin wannan furuci ba, yana mai cewa, ba a horar da ‘yan wasansa akan irin wannan dabi’a ba.
A can baya, an zargi Guardiola da yi wa 'yan wasan hudubar yi wa abokan karawarsu mugunta cikin dabara, zargin da ya musanta.
A bangare guda, Guardiola ya ce, a yanzu, gidan Manchester United wato Old Trafford, ba wurin da za a ji tsoron ziyarta bane, sabanin shekarun baya da ake fargabar kai mata ziyara.
Muddin Manchester City ta yi nasara a wasan na yau, hakan zai dada kara mata kwarin guiwar ci gaba da rike kambin firimiyar Ingila.
Alkaluma sun nuna cewa, Manchester City ta samu nasara a wasanni biyar daga cikin bakwai da ta buga a Old Trafford a baya-bayan nan.
A karon farko tun shekarar 1989, Manchester United ta yi rashin nasara a wasanni shida daga cikin takwas da ta buga a gasa daban daban a baya-bayan nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu