Wasanni

Manchester City na jin kamshin kofin firimiya

Mai horar da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola. REUTERS/David Klein

Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester City ta koma saman teburin gasar firimiyar Ingila bayan ta doke Manchester United da ci 2-0 a Old Trafford, in da a yanzu ta bai wa Liverpool tazarar maki guda.

Talla

Manchester City ta zura kwallayen ne ta hannun Bernardo Silva da kuma Leroy Sane a minti na 54 da kuma 66 bayan dawowa daga htuun raboin lokaci.

A karo na bakwai kenan da Manchester United ke shan kashi a wasanni tara da ta buga a baya-bayan nan.

Yanzu haka wasanni uku uku suka rage wa Manchester City da Liverpool, yayinda Pep Guardiola ya shawarci ‘yan wasansa da su yi barci sosai, su kuma kaurace wa kallon talabijin don kintsawa fafatawar da za su yi da Burnley a ranar Lahadi mai zuwa, kafin daga bisani su sake kece raini da Leicester City da Brighton.

Dama dai ana ganin babban wasan da ke gaban Guardiola, shi ne karawar da suka yi da Manchester United kuma ya samu nasara.

A gobe Juma’a  Liverpool za ta kece raini da Huddersfield.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI