Wasanni-Gasar Zakarun Turai

UEFA ta haramtawa Neymar doka wasannin gasar zakarun Turai 3 a badi

Dan wasan gaba na PSG Neymar Junior
Dan wasan gaba na PSG Neymar Junior REUTERS/Charles Platiau

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta sanar da matakin haramtawa dan wasan gaba na PSG Neymar Junior doka wasannin cin kofin zakarun Turai 3 a kaka mai zuwa, bayan samunsa da laifin wallafa kalaman cin mutuncin alkalin wasa, yayin karawarsu da Manchester United cikin watan jiya.

Talla

A wasan wanda da shi ne United ta fitar da PSG daga gasar ta cin kofin zakarun Turai bayan ratata mata kwallaye har 3 da 1, Neymar wanda bai taka leda a wasan ba saboda jinyar karaya a tafin kafa da ya ke, ya bayyana alkalan da suka kula da wasan a matsayin wadanda basu san aikinsu ba.

Cikin wasu bayanai da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Neymar bayan kammala wasan ya ce an sanya mutanen da basu san meye kwallo ba yin alkalanci a wasan, su yi duk abin da za su yi.

Bisa tanadin dokar, hukumar ta UEFA dai furta makamantan kalaman da ga bakin dan kwallo kan jam asa haramcin doka wasu adadin wasanni.

Yanzu haka dai, Neymar ba zai samu damar doka wasanni 3 karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai a kaka mai zuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.