Wasanni

An sayar da takalmin kwallon Pogba akan Naira miliyan 12

Paul Pogba na Faransa bayan lashe kofin duniya a Rasha
Paul Pogba na Faransa bayan lashe kofin duniya a Rasha REUTERS/Michael Dalder

Takalmin kwallon da dan wasan Faransa, Paul Pogba ya buga gasar cin kofin duniya da shi a Rasha a bara, an sayar da shi akan farashin Euro dubu 30, kwatankwacin Nairar Najeriya, miliyan 12 da dubu 60 a wani bikin baje koli da aka gudanar a birnin Paris.

Talla

Pogba na Mancheter United, wanda kuma ya ci kwallo ta uku a wasan da Faransa ta doke Croatia da 4-3 a gasar ta cin kofin duniya, ya sadaukar da kudin takalmin ga gidauniyar agaji don taimaka wa daliban makarantun boko da ke cikin tsanani.

Tun da farko, masu shirya bikin baje kolin sun yi hasashen cewa, farashin talakimin na Pogba zai kai Euro dubu 35 zuwa dubu 50.

Kazalika an sayar da wata rigar kwallo da Pogba din ya sanya ta a karawar da Faransa ta casa Icelaland a matakin wasan gab da na kusan karshe a gasar cin kofin kasashen Turai ta 2016 akan farashin Euro dubu 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.