Wasanni-Gasar Zakarun Turai

Ba ni da shakku a wasanmu na yau -Pochettino

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino Reuters/Hannah McKay Livepic

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino ya yi ikirarin cewa nasara ko akasinta a wasansu na yau da za su karbi bakonci Ajax ya dogara ne ga jajircewar ‘yan wasansa wanda ya ce kwazon da suka nuna ne ya kai Club din wannan mataki karon farko a tarihinsa.

Talla

A cewar Pochettino ba zai yi danasanin ko maye zai faru a wasan na yau ba, wanda shi ne zagayen farko na wasan gab da na karshe na cin kofin zakarun Turai, amma dai ya na fatan su samu gagarumar nasara a wasan.

Tottenham din ce dai za ta karbi bakoncin Ajax wadda ta fitar da Real Madrid a zagayen kungiyoyi 16 ka na ta fitar da Juventus a zagayen kungiyoyi 8.

Ajax dai ta jima rabonta da kaiwa wannan mataki, sai dai a wannan karon irin salon da ta shigo gasar da shi na nuna cewa za ta iya nasarar hatta lashe kofin.

A bangare guda ita kuma Tottenham wannan ne karon farko a tarihinta da ta ke ka iwa wasan gab da na karshen, ko da dai ta yi nasarar ka iwa wasan gab da na karshe na cin kofin Turai a shekarar 1962 amma kuma ta yi rashin nasara a hannun Benfica.

Tottenham dai ta yi nasara kan Manchester City ne da kwallaye 4 da 3 makwanni 2 da suka gabata, matakin da ya bata damar kaiwa wannan matsayin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.