Wasanni-kwallon kafa

Salah ya taya Virgil murnar lashe kyautar gwarzon dan wasan Ingila

Muhamad Salah
Muhamad Salah REUTERS/Andrew Yates

Dan wasan gaba na Liverpool Mohammed Salah ya taya abokinsa Virgil van Dijk murnar lashe kyautar gwarzon dan wasan Ingila a bana, sai dai ya gargade shi kan kada kyautar ta rude shi wajen yin sakaci da sauran wasannin da suka rage musu.

Talla

Salah wanda ya lashe makamanciyar kyautar a bara, shi ne dan wasa na farko da ya aike da sakon taya murnar ga van Dijk dan Holland, tun kafin a sanar da nasarar ta sa a hukumance, inda ya wallafa hoton Van Dijk a shafinsa na Twitter tare da alamun murna da kuma rubutun da ke cewa ka kula fa, kuma ka da ka lashe kayutaukan bana duka, inba haka ba kasan mai ze faru shekara mai zuwa.

Virgil van Dijk ya yi nasarar lashe kyautar ne bayan doke takwaransa na Liverpool din Sadio Mane, kana ‘yan wasan Manchester City irinsu Bernardo Silva, da Raheem Sterling da kuma Sergio Aguero, ka na Eden Hazard na Chelsea.

Salah wanda ba ya cikin jerin ‘yan wasan da suka shiga jerin lashe kyautar a bana duk da cewa yana cikin jerin ‘yan wasa mafi zura kwllaye bayan zura kwallo 25 cikin wannan kaka, sai dai ana ganin akwai yiwuwar ya iya sake lashe kyautar takalmin zinare saboda kwazonsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI