Isa ga babban shafi
Wasanni

Yan wasan Real Madrid sun ki goyon bayan shirin sayen Pogba

Dan wasan Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba. Reuters / Carl Recine Livepic
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Rahotanni daga Real Madrid sun ce ‘yan wasan kungiyar da dama sun bayyana rashin goyon bayan zuwan dan wasan Manchester United Paul Pogba, wanda ake sa ran kungiyar za ta saya a karshen kakar wasa ta bana.

Talla

Pogba na cikin manyan ‘yan wasan da kocin Real Madrid Zinaden Zidane ke fatan saya don karfafa kungiyar, wadda ta fuskanci koma baya matuka a kakar wasa ta bana.

Zalika shi kansa Pogba, majiyoyi masu tushe sun rawaito cewa, a shirye yake ya sauya sheka daga United don komawa karkashin Zidane.

Sai dai yayin da ‘yan wasan Real Madrid suka amince cewar zuwan dan wasan Chelsea Eden Hazard cikinsu, zai taimaka matuka wajen samun nasarori, mafi akasarinsu basu gamsu da kwarewar Pogba, dan haka suke ganin zuwansa bashi da amfani.

A kakar wasa ta bana dai Paul Pogba ya ci wa Manchester United kwallaye 13, ya kuma taimaka wajen jefa wasu kwallayen guda 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.