Zan koma aikin horaswa bayan yin ritaya daga kwallon kafa - Ronaldo
Wallafawa ranar:
Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo, ya ce bayan yin ritaya daga buga kwallon kafa, zai ci gaba da kasancewa cikin duniyar kwallon ta hanyar shiga aikin horaswa.
Ronaldo ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wata kafar yada labaran Birtaniya, wadda ta nemi sanin abinda zai yi bayan daina murza leda.
Ronaldo wanda ya kafa tarihin zama dan wasan da ke kan gaba wajen yawan kwallayen a Real Madrid, ya taimakawa kungiyarsa ta yanzu wato Juventus, wajen lashe kofin kasar Seria A ta Italiya makwanni 2 da suka gabata.
Cristiano Ronaldo ya kuma kafa tarihin zama dan wasa na farko a duniyar kwallon kafa da ya taimakawa kungiyoyin da ya bugawa, da suka hada da Manchester United, Real Madrid da kuma Juventus, wajen lashe kofunan gasar kasashen da suke, a Ingila, Spain, da kuma Italiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu