Wasanni

United ta rasa damar halartar gasar zakarun Turai

Paul Pogba cikin jimami, bayan wasan da suka tashi 1-1 da Huddersfield.
Paul Pogba cikin jimami, bayan wasan da suka tashi 1-1 da Huddersfield. The Independent

Burin Manchester United na samun damar halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a badi ya kawo karshe, bayan wasan da suka fafata da kungiyar Huddersfield na gasar Premier a jiya Lahadi.

Talla

Duk kokarin da United ta yi na neman nasara a wasan ya ci tura, inda aka tashi 1-1.

A wasan na jiya dai Huddersfield ta kawo karshen rashin nasarar da ta rika fuskanta a wasanni takwas da ta buga a jere, koda yake ta sauka daga ajin gasar Premier mai daraja ta daya, kasancewarta a karshen jerin kungiyoyin da suka fafata a gasar ta bana.

A bangaren Manchester United kuwa, wasanni biyu kenan ta samu nasara kawai daga cikin 11 da ta fafata jere da juna a dukkanin wasannin da ta buga a ciki da wajen gasar Premier a baya bayan nan.

Gazawa wajen doke Huddersfieled da United ta yi, yasa wasu soma diga ayar tambaya kan kwarewar mai horas da kungiyar Ole Gunnar Solksjear, wanda aka tabbatar da shi a matsayin kocinta na dindindin a cikin watan Maris da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI