Wasanni

FIFA ta kara yawan kyautukan da za ta rika baiwa mata

Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino. REUTERS/Naseem Zeitoon/File Photo

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta bayyana kikirar wasu karin kyautuka guda biyu da za ta rika baiwa aijin mata a fagen kwallon kafa.

Talla

Matakin a cewar FIFA, zai tabbatar da daidaito tsakanin bangaren maza da mata a fagen na kwallon kafa.

Sabbin kyautukan da hukumar ta kara sun hada da karrama mace mai tsaron raga da ta yi fice, sai kuma karrama tawagar kwallon kafar ta mata, mafi kwazo yayin bikin kyautuklan da take badawa a duk shekara.

Bikin bayar da kyautukan hukumar FIFA na wannan shekara zai gudana a birnin Milan, ranar 23 ga watan Satumba.

A ranar 7 ga watan Yunin wannan shekara kuma za a soma gudanar da gasar cin kofin duniya ta mata a kasar Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI