Isa ga babban shafi
Wasanni

Juventus za ta raba gari da kocinta

Kocin Juventus Massimiliano Allegri.
Kocin Juventus Massimiliano Allegri. Reuters/Giorgio Perottino
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Kocin Juventus Massimiliano Allgeri ya yanke shawarar rabuwa da kungiyar bayan karkare kakar wasa ta bana, bayan shafe shekaru 5 yana horar da zakarun na gasar Seria a Italiya.

Talla

Jaridar La Stampa ta kasar Italiya da ake wallafa ta a birnin Turin ce ta rawaito cimma yarjejeniyar rabuwar da Allegri yayi da Juventus, ko da yake ba ta yi karin bayani akan abinda yarjejeniyar ta kunsa ba.

A baya dai kungiyoyin Chelsea da Arsenal sun yi kokarin daukar hayar kocin na Juventus mai shekaru 51, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

A halin yanzu kuma kungiyar Paris saint germain ke neman daukar Massimiliano Allegri, don maye gurbin kocinta Thomas Tuchel da take shirin kora.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.