Wasanni

Kungiyoyin Ingila sun kafa tarihi irinsa na farko

Kungiyoyin Ingila hudu za su kara a wasannin karshe na gasar zakarun Turai da kuma Europa
Kungiyoyin Ingila hudu za su kara a wasannin karshe na gasar zakarun Turai da kuma Europa REUTERS/Emmanuel Foudrot

A karon farko kungiyoyin Ingila guda hudu za su buga wasannin karshe a a gasar Europa da kuma gasar zakarun Turai na bana, inda Chelsea za ta hadu da Arsenala  Europa, yayinda Liverpool za ta hadu da Tottenham a zakarun Turai.

Talla

Chelsea ta tsallaka zuwa makin wasan karshe ne a gasar Europa, bayan da ta samu nasarar doke Frankfurt a bugun fanariti da kwallaye 4-3 a zagaye na biyu na matakin wasan dab da na kusan karshe.

An yi bugun fanaritin ne sakamkon kunnen doki 1-1 da kungiyoyin biyu suka yi.

Chelsea za ta hadu da Arsenal a wasan karshe da za a gudanar a Baku, babban birnin Azerbaijan a ranar 29 ga wannan wata na Mayu.

Arsenal ta samu damar zuwa wasan karshen ne bayan da ta casa Valencia da ci 4-2 a zagaye na biyu na matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar ta Europa.

A bana dai, kungiyoyin kwallon kafa na Ingila sun nuna bajinta matuka, ganin yadda suka yi wa takwarorinsu na sauran kasashen Turai zarra, domin kuwa ko a gasar zakarun Turai, Liverpool da Tottenham za su buga wasan karshe a ranar 1 ga watan mai zuwa a birnin Madrid.

A bangare duda, an bai wa Arsenal da Chelsea kowacce daga cikinsu tikiti dubu 6 na wasan karshen a Baku, a filin wasan da ke daukar nauyin mutane dubu 68 da 700.

Sai dai Arsenal ta bayyana adadin da aka ware mata a matsayin abin kunya, abinda ta ce, zai jefa kungiyar cikin tsaka mai wuya, lura da dubun dubatan magoya bayanta.

Su kuwa, kungiyoyin Liverpool da Tottenham an ware musu tikiti dubu 16 da 613 ne kowacce, domin sayar wa magoya bayansu da za su halarci wasan karshe a gasar zakarun Turai a filin wasa na Wanda Metropolitano mai daukar nauyin mutane dubu 68 a birnin Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.