Wasanni

PSG za ta sayi 'yan wasan Real Madrid 3 a lokaci guda

Wasu daga cikin manyan 'yan wasan Real Madrid Toni Kroos, Isco, da kuma Gareth Bale.
Wasu daga cikin manyan 'yan wasan Real Madrid Toni Kroos, Isco, da kuma Gareth Bale. REUTERS

Kungiyar PSG ta soma yunkurin ganin ta sayi wasu 'yan wasan Real Madrid guda uku da zarar an bude fagen hada-hadar sauyin shekar ‘yan wasa. 

Talla

Jaridar Le Parisien da ke Faransa, ta rawaito cewa 'yan wasan sun hada da, Toni Kroos, Isco, da kuma Gareth Bale, kuma kungiyar ta PSG, ta ce a shirye take ta mikawa Real Madrid euro miliyan 180, domin saye su a lokaci guda.

A baya bayan nan dai Gareth Bale ya rasa damar da yake samu a Real Madrid na zama dan wasan da ake ji dashi, tun bayan da Zinaden Zidane ya sake karbar mukamin horar da kungiyar a yan watannin da suka gabata, hakan tasa ake alakanta dan wasan komawa wasu kungiyoyi, ciki harda Manchester United.

A makon nan ne kuma Real Madrid ta gabatarwa da kungiyar Tottenham tayin mika mata tsohon wasanta Gareth Bale a matsayin aro kan euro miliyan 10.

A shekarar 2013, Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham kan euro miliyan 86, abinda ya sa shi zama dan wasa mafi tsada a waccan lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.