Wasanni

Formiga ta zama yar wasa mafi tsufa a gasar cin kofin duniya

Yar wasan Brazil Formiga mai shekaru 41, za ta jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2019, ajin mata da Faransa za ta karbi bakunci.
Yar wasan Brazil Formiga mai shekaru 41, za ta jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2019, ajin mata da Faransa za ta karbi bakunci. Frederick Breedon/Getty Images

‘Yar wasan kwallon kafa ta kasar Brazil Formiga da ke bugawa kungiyar PSG, ta kafa tarihin zama yar wasa ta farko a ajin mata, da za ta wakilci kasar ta a gasar cin kofin duniya sau 7.

Talla

Idan Formiga ta samu buga wasannin gasar cin kofin duniyar da Faransa za ta karbi bakunci, za ta kuma kafa tarihin zama ‘yar wasa mace mafi yawan shekaru da za ta bayyana a gasar, la’akari da cewa a yanzu haka Formiga na da shekaru 41.

A shekarar 1995 Formiga ta soma bugawa kasarta Brazil wasanni, a lokacin da take da shekaru 17.

Brazil ta tsinci kanta cikin rukuni na 3, inda za ta fafata da kasashen Jamaica, Italiya da kuma Australia, a gasar cin kofin duniyar da za a soma a ranar 7 ga watan Yuni,

Duk da cewa Brazil ta halarci dukkanin gasar cin kofin duniya guda 7 da aka shirya, har yanzu kasar ta gaza daukar kofi, zalika a shekarar 2007 ne kawai, kasar ta Brazil ta kai zagayen karshe, inda kuma Jamus ta doke ta, yayin gasar da China ta karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.