Isa ga babban shafi
Wasanni

Solksjaer na tare da cikakken goyon bayan mu - United

Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer.
Mai horas da kungiyar Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer. Reuters/Lee Smith
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Shugaban Manchester United Ed Woodward, yace za su baiwa kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer isassun kudade, da kuma dukkanin goyon bayan da yake bukata, wajen sayen ‘yan wasa, domin maido martabar da kungiyar ta rasa.

Talla

Manchester United dai ta kammala gasar Premier ta bana a matsayin kungiya ta 6, da maki 66, tazarar maki 32 tsakaninta da takwararta Manchester City, wadda ta lashe kofin Premier na bana da maki 98.

Bayan karbar ragamar horar da United daga Jose Mourinho, Ole Gunnar Solkjaer, ya soma da kafar dama, bayanda kungiyar ta lashe wasanni 14 daga cikin 17 na farko da ta fafata a karkashinsa.

Sai dai daga bisani a karshen kakar wasa ta bana, kungiyar ta rasa karsashinta, domin wasanni 2 kawai ta iya lashewa daga cikin 12 da ta fafata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.