Arsenal za ta mika 'yan wasa 3 don sayen tauraron Crystal Palace
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni sun ce Arsenal ta gabatarwa da Crystal Palace wasu ’yan wasanta uku, a kokarin sun sayi tauraron kungiyar Wilfred Zaha.
Yunkurin na Arsenal ya zo ne adai dai lokacin da Zaha ya bayyana aniyarsa ta neman rabuwa da Crystal Palace, wanda kuma aka dade ana alakanta shi da sauya sheka zuwa Arsenal.
Tuni dai Crystal Palace ta sanya farashin euro miliyan 80 kan Zaha, sai dai ana ta bangaren, Arsenal ta mika tayin biyan euro miliyan 40 ne kawai,hakan tasa kungiyar hadawa da kari ‘yan wasanta guda uku.
Jaridar the Sun da ke Birtaniya ta rawaito cewa, bayaga kudi, yan wasan da Arsenal ke son mikawa don samun nasarar sayen Wlifred Zaha sun hada da Carl Jenkinson, Reiss Nelson da kuma Calum Chambers.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu