Wasanni

Manchester City ta kafa tarihi irinsa na farko a Ingila

Tawagar 'yan wasan Manchester City yayin murnar nasarorin da suka samu a kakar wasa ta bana (2018/2019).
Tawagar 'yan wasan Manchester City yayin murnar nasarorin da suka samu a kakar wasa ta bana (2018/2019). Reuters/John Sibley

Manchester City ta kafa tarihi irinsa na farko a Ingila, bayan da a ranar Asabar ta lashe kofin gasar FA a filin wasa na Wembley inda ta casa Watford da kwallaye 6-0.

Talla

‘Yan wasan City da suka hada da David Silva, Kevin de Brunyne, gabriel Jesusu, da kuma Raheem Sterling ne suka jeffa kwallayen 6, wadanda Sterling ya ci uku daga ciki.

Nasarar ta ranar Asabar ta baiwa Manchester City damar zama kungiya ta farko a Ingila da ta lashe dukkanin kofunan gasar cikin gida da ta fafata cikinsu, da suka hada da kofin gasar Premier, FA da kuma League Cup ko Carabao, dukkaninsu a kakar wasa ta bana.

Kocin na Manchester City Pep Guardiola ya bayyana cewa lashe wadannan kofuna a kakar wasa daya, ya fi lashe kofin gasar Zakarun Turai wahala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.