Wasanni

Messi ya goge tarihin shekaru 66

Kaftin din Barcelona Lionel Messi .
Kaftin din Barcelona Lionel Messi . REUTERS/Sergio Perez

Kaftin din Barcelona Lionel Messi ya sake lashe kyautar dan wasan da ya ci kwallaye mafi yawa a gasar La Liga, karo na uku a jere, sau 6 kuma a jimlace.

Talla

Messi ya lashe kyautar da ake yiwa lakabi da Pichichi bayan cin dukkanin kwallaye biyu a wasan da suka tashi 2-2 tsakaninsu da Eibar a ranar Lahadi, inda ya kammala kakar wasa ta bana a gasar ta La Liga da yawan kwallaye 36.

Hakan ya baiwa kaftin din na Barcelona kafa irin tarihin da dan wasan Athletic Club Telmo Zarra yayi shekaru 66 da suka gabata.

A gefe guda kuma Messi ya kafa tarihin zama dan wasa na farko da ya baiwa takwarorinsa tazarar kwallaye mafi yawa a kakar wasa guda.

A kakar wasa ta bana dai Messi ya baiwa wadanda ke biye da shi, Karim Benzema da Luis Suarez tazarar kwallaye 15, wanda rabon da irin haka ta auku tun a shekarar 1987, lokacin da tsohon dan wasan Real Madrid Hugo Sanchez ya yiwa abokan wasansa zarra a fagen yawan zura kwallaye da tazarar guda 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.