Najeriya-Wasanni

Super Falcons ta Najeriya ta lashe kofin WAFU

'Yan wasan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya bangaren mata super Falcons
'Yan wasan tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya bangaren mata super Falcons Premium Times Nigeria

Kungiyar kwallon kafar Najeriya bangaren mata Super Falcons ta yi nasarar lashe gasar cin kofin kasashen yammacin Afrika da ya gudana a Ivory Coast bayan lallasa mai masaukin baki a wasan karshe da kwallaye 5 da 4.

Talla

Yayin wasannin gasar da ta gudana tsakanin kasashen 8 na yankin yammacin Afrikan, Super Falcons ta kafa tarihin kammala wasannin ba tare da ta yi rashin nasara a hannun kowacce kungiya ba.

Tuni dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya aikewa tawagar da sakon taya murnar lashe kofin, inda ya bukace su da ci gaba da nuna hazaka a wasannin gasar cin kofin duniya da ke tafe cikin shekarar nan a Faransa, gasar da tuni Super Falcons ta samu tikitin zuwanta, tun bayan dage kofin Afrika watannin baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI