Wasanni

Real Madrid: Bale ya shirya zama 'kwalam ta koki mai ganin man dutse'

Gareth Bale.
Gareth Bale. REUTERS/Wolfgang Rattay

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale, ya bukaci kungiyar ta biya shi euro miliyan 15, muddin tana bukatar ya rabu da ita cikin sauki a karshen kakar wasa ta bana, ba tare da daukar lokaci ba.

Talla

Bale ya bayyana matsayinsa ne bayan da kocinsa Zinaden Zidane ya ce zai iya barin kungiyar da zarar an soma hada-hadar sauyin shekar yan wasa, in kuwa ba haka ba zai ci gaba da zaman dumama kujera ko benci.

Kocin na Real Madrid dai ya ki baiwa Bale damar buga wasan karshe na gasar La Liga da Real Betis ta lallasa su har gida da kwallaye 2-0.

Sai dai duk da cewa Bale ya fusata da yadda Zidane ke maida shi saniyar ware, da alama dan wasan na kokarin zama 'kwalam ta koki mai ganin man dutse', domin kuwa wata majiya da ke kusa da shi, ta ce ya shaidawa abokan wasansa cewa a shirye yake, ya ci gaba da zama tare da Real Madrid ko da kuwa zai ci gaba da dumama kujera, har zuwa lokacin da yarjejeniyarsa da kungiyar za ta kare nan da shekaru 3, inda zai rika amsar euro miliyan 15 a duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.