Wasanni-Kwallon kafa

Liverpool na shirin sayen dan wasan Najeriya

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samuel Chukwueze
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samuel Chukwueze NAN

Dan wasan kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles Samuel Chukwueze na cikin jerin ‘yan wasa 12 da Liverpool ke fatan saya a cikin kakar nan.

Talla

Chukwueze mai shekaru 19 na cikin matasan ‘yan wasa ‘yan Afrika da ke taka leda a Turai inda aka ittifakin darajarsa ta kai yuro miliyan 30.

Chukwueze wanda ya taba dokawa Super Eagles wasa sau daya ya taka leda har sau 46 a bangaren Villarreal inda ya zura kwallaye 10 ya kuma taimaka aka zura 4.

Sauran ‘yan wasan ajin farko da Liverpool ta nuna sha’awar sayensu sun hada da Bertrand Traore da Maxwell Cornet da kuma Ryan.

Sauran rukuni na biyu na ‘yan wasan da Liverpool ke fatan saya akwai Hakim Ziyech na Ajax da Timo Werner da Joao Felix da Nicolas Pepe sai Julian Brandt, da David Neres kana Maxi Gomez sannan Felipe Anderson.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.